IQNA

Saudiyya Na Ci Gaba Da Tsare Jiragen Da Suke Dauke da Taimako Zuwa Yaman

22:37 - July 01, 2020
Lambar Labari: 3484940
Tehran (IQNA) ci gaba da tsare manyan jiragen ruwa da suke dauke da makamashi tare da hana su isa kasar Yemen, hakan na yin barazana ga rayuwan al’ummar kasar.

Ma’aikatar lafiya ta kasar ta Yemen ta sanar da cewa, ci gaba da tsare manyan jiragen ruwa da suke dauke da makamashi tare da hana su isa kasar Yemen, hakan na yin barazana ga rayuwan al’ummar kasar.

Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Yemen ta fitar a yau ta sanar da cewa, Saudiyya da Amurka suna ci gaba da tsare manyan jiragen ruwa da suke dauke da makashi zuwa kasar Yemen tsawon watanni.

Bayanin ya ce a cikin jiragen ruwan akwai man fetur da dangoginsa da kuma iskar gas, wadanda al’ummar kasar ta Yemen suke da matukar bukatuwa zuwa gare su, amma jiragen suna tsaye a cikin ruwa an hana su motsawa.

Haka nan kuma bayanin ma’aikatyar kiwon lafiyar ta kasashen Yemen, baya ga yadda wannan lamari yake shafar rayuwar jama’a kai tsaye ta fuskancin hidimominsu da sarrafa abinci, a lokaci guda yana shafar batun lafiya, domin akwai kayan da ake yin amfani da su a bangaren kiwon daga cikin kayan da aka tsare.

Ko a jiya Saudiyya ta kaddamar da wasu hare-hare a yankin Ma’arib da ke yammacin kasar ta Yemen, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula, yayin da dakarun kasar gami da mayakan sa kai na larabawan kasar da suka hada da kungiyar Ansarullah (Alhuthi) suka sha alwashin mayar da martani.

Ko a yau kawancen Saudiyya da ke kai hare-hare kan Yemen, ya sanar da cewa zai fara kaddamar da wasu sabbin hare-haren a kan al'ummar kasar ta Yemen, da sunan yaki da mayakan kungiyar Ansarullah (Alhuthi).

3907920

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen ، saudiyya ، Amurka ، killace ، tsare ، jiragen ruwa ، taimako ، makamshi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha