IQNA

Bayani Kan Sheikh Hani Alhusaini:

Makarancin Kur’ani Dan Masar Da Ya Zo Na Daya A Gasar Kur’ani Ta Malaysia

22:14 - July 15, 2020
Lambar Labari: 3484988
Sheikh Hani Alhusaini ya fara bayyana a idon duniya a lokacin da ya lashe gasar kur’ani ta kasar Malaysia a shekara ta 2010.

A wata zantawa da ya yi da shafin yada labarai na sadal balad sheikh Hani Alhusaini ya bayyana cewa, ya hardace kur’ani mai tsarki ne tun yana dan shekaru 19 da haihuwa.

Ya ci gaba da cewa, a cikin shekara ta 2020 ne aka dauke shi a matsayin mai karatu a hukumance a gidan radiyo da talabijin na kasar Masar, kuma tun daga lokacin ne ya fara halartar manyan tarukan karatun kur’ania  kasashen duniya.

Ya ce ya samu tarbiya ne tun daga gidansua  gaban mahaifansa, bayan nan kuma ya samu wata tarbiyar da karatua  gaban manyan malamansa da suka hada da sheikh Abul Ainain Shu’aisha.

Bayan nan kuma ya ci gab ada harkokinsa na koyar da dalibaia  makarantu daban-daban a cikin kasar ta Masar, domin samun albarkar kur’ani mai girma ta hanyar koyar da wasu abin da ke cikinsa.

Ya kara da cewa, ya kasance mai shaukin kur’ani tun yana karami, kuma Allah ya albarkaci rayuwarsa da karatunsa da kuma hardarsa, tare das aka dukkanin lokacinsa a cikin lamarin kur’ani.

3910632

 

 

captcha