IQNA

Gwamnatin Malaysia Ta Bayar Da Taimakon Kudi Fiye Da Dala Miliyan 4 Ga Cibiyoyin Musulmi

20:23 - July 28, 2020
Lambar Labari: 3485031
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Malaysia ta bayar da taimakon kudi fiye dad ala miliyan hudu ga cibiyoyin musulmi 1830 a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Bernama ya bayar da rahoton cewa, Zulkif Muhammad Bakri ministan kula da harkokin addini na kasar Malaysia ya bayyana cewa; daga 30 ga watan Yuni ya zuwa yanzu, sun bayar da taimakon kudi ringit miliyan 18 kwatankwacin dala miliyan 4.230, ga cibiyoyin musulmi na kasar.

Ya ce an kafa wannan asusu ne da nufin tallafawa cibiyoyin musumi da suke da matsaloli sakamon bullar cutar corona, wadda ta kawo tsaiko a cikin abubuwa da dama.

Ya kara da cewa, baya ga cibiyoyin addinin muslunci, hatta wasu cibiyoyi na addinin buda da ke kasar an taimaka musu a cikin irin wannan yanayin.

Tun a ranar 24 ga watan Maris na wannan shekara ne dai gwamnatin Malyasia ta kafa wannan asusu, da nufin yin amfani da kudaden da yake Tarawa wajen taimaka ma cibiyoyin addinin muslunci da makarantu.

3913155

 

Abubuwan Da Ya Shafa: gwamnatin Malyasia ، shekara ، cibiyoyin addini ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha