IQNA

An Yi Kira Da A Saki Sheikh Ibrahim Zakzaky

22:20 - July 29, 2020
Lambar Labari: 3485033
Tehran (IQNNA) Kwamitin kare hakkokin musulmi da ke da mazauni a birnin Landan an kasar Burtaniya, ya yi kira da a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran Harkar Islamiyya da ake tsare da shi a Najeriya.

A cikin wani sako na budaddiyar wasika kwamitin kare hakkokin musulmi ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta saki Sheikh Ibrahim Zakzaky tare da maidakinsa da ake tsare da su.

Sakon ya ce; bisa la’akari da cewa tun kafin wannan lokaci akwai kiraye-kiraye da dama da ke neman sakin Malamin da maidakinsa da ake tsare da su tun 2015, da hakan ya hada har da kiran da kotun tarayyar ta Najeriya ta yi kan hakan, a bisa wannan, kwamitin kare hakkokin musulmin yana kara jaddada kira da a saki Sheikh zakzaky da maidakinsa.

Wannan kira dai yana zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran a gobe Alhamis 30 ga watan Yuli, kotun Kaduna za ta sake gudanar da zama domin sauraren shari’arsa tare da malama Zeenat.

Kotun tarayya ta bayar da umarnin sakin Sheikh Zakzaky tare da maidakinsa a cikin shekara ta 2016, tare da biyansu tarar kudi, amma har yanzu ana ci gaba da tsare su, bisa tuhumar tayar da hargitsi da kuma kashe jami’in tsaro guda, zargin da Malamin da maidakinsa ba su amince da shi ba.

A karshen shekara ta 2015 ne jami’an soji suka kaddamar da hari a kan cibiyar tarukan Harka Islamiyya ta Husainiyar Baqiyataollah a Zariya, bisa hujjar cewa an tare wa babban Hafsan sojin kasa hanya, inda suka kashe mutane a wurin, bayan nan kuma suka kai farmaki kan gidan Shiekh Zakzaky a unguwar Gyallesu da ke Zaria, inda a nan ma suka kashe mutane da dama, daga ciki har da ‘ya’yansa uku da kuma ‘yan uwansa na jini, inda gwamnatin Kaduna ta yi ikirarin cewa ta bizne gawawwakin mutane 347 daga cikin wadanda aka kashe a wurin, yayin da majiyoyin Harka Islamiyya ke cewa adadin wadanda sojoji suka kashe ya haura mutane dubu daya.

3913333

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha