IQNA

Za A Bude Masallatai A Kasar Aljeriya

23:13 - August 04, 2020
Lambar Labari: 3485055
Tehran (IQNA) shugaban Aljeriya ya sanar ce, kasarsa na duba yuwuwar sake bude masallatai ga jama'a,

Shafin yada labarai na almisrawi ya habarta cewa, shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune, ya sanar ce, kasarsa na duba yuwuwar sake bude masallatai ga jama'a, da suka kasance a garkame yau kusa da watannin biyar sakamakon matakan yaki da annobar korona.

Shugaba Tebboune ya umarci Firaminista Abdelaziz Djerad, ya shirya bude masallatan sannu a hankali.

Ya kara da cewa, da farko, shirin zai bude manyan masallatai dubu dayawanda zai bada damar bayar da tazara tsakanin mutane, sannan dole ne kowa ya sanya takunkumin rufe baki da hanci.

Aljeriya dai na daga cikin kasashen da cutar korona ta fi wa illa a Afrika, inda alkalumman wadanda suka kamu ya kai dubu talatin sai kuma sama da dubu daya da cutar ta yi ajalinsu.

 

3914664

 

Abubuwan Da Ya Shafa: aljeriya cutar corona kasar alkalumma kasashe
captcha