IQNA

Tilawar Karim Mansuri A Wurin Taron Addu’ar Kwanaki 7 Da Rasuwar Ayatollah Taskhiri

22:37 - August 25, 2020
Lambar Labari: 3485117
Tehran (IQNA) fitaccen makarancin kur’ani dan kasar Iran Karim mansuri ya gabatar da tilawar kur’ani a wurin taron addu’ar kwanaki bakwai da rasuwar Ayatollah Taskhiri.

A yau ne aka gudanar da taron addu’ar kwanaki bakwai da rasuwar Ayatollah Taskhiri, inda fitaccen makarancin kur’ani dan kasar Iran Karim mansuri ya gabatar da tilawar kur’ani a wurin, tare da halartar manyan mutane daga ciki har da Abu Zar Ibrahimi Torkamani, shugaban hukumar yada al’adun musulunci.

Karim Mansuri dai yana daga cikin fitatattun makaranta kur’ani a  duniya, wanda ya sha lashe gasar kur’ani ta duniya a lokacin kuruciyarsa, inda a halin yanzu yake koyarwa a cibiyoyin ilimi daban-daban na kasar Iran.

3919040

 

 

 

 

captcha