IQNA

23:29 - August 29, 2020
Lambar Labari: 3485132

UAE Ta Soke Dokar Hana Alaka Da Isra’ila

Tehran (IQNA) hadaddiyar daular larabawa ta soke dokar haramta alaka da Isra’ila.

UAE Ta Soke Dokar Hana Alaka Da Isra’ila

Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa UAE, Khalifa Bin Zayed al- Nahyan ya soke dokar da ta hana yin alaka ta kasuwanci da tattalin arziki da haramtacciyar ƙasar Isra’ila a ci gaba da ɗaukar matakan ƙulla alaƙa tsakanin ƙasarsa da Haramtacciyar ƙasar Isra’ilan.

A yau Asabar ne Kamfanin dillancin labaran UAE ɗin ya bayar da labarin cewa a wata doka da ya fitar a yau ɗin nan Khalifa Bin Zayed Al Nahyan ya ba da umurnin soke dokar da ta hana mu’amala ta kasuwanci da Isra’ilan wanda a halin yanzu hakan zai ba da damar ƙulla alaƙoƙi na kasuwanci tsakanin UAE din da Isra’ila.

A ranar 13 ga watan Augustan nan ne dai shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa UAE da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar ƙulla alaƙa a tsakaninsu a matakin farko na ci gaba da ƙoƙarin da ake yi na ganin sauran ƙasashen larabawa sun shigo sahu.

Wannan sanarwa dai ta fuskanci tofin Allah tsine daga ɓangarori daban-daban na duniyar larabawa da na musulmi.

 

 

3919707

 

 

 

 

captcha