A jiya an gudanar da taruka a kasar Lebanon tare da halartar manyan jami’an gwamnati, daga ciki har da shugaban majalisar dokokin kasar Nabih Birri da kuma wasu ‘yan majalisa gami da ministoci, domin tunawa da cikar shekaru 42 da bacewar Imam Musa Sadr a kasar Libya.
Imam Musa Sadr shugaban kungiyar Amal kuma shugaban majalisar koli ta mabiya mazhabar shi’a akasar Lebanon, ya bace ne a ranar 31 ga watan Augustan 1978 a kasar Libya a yayin wata ziyarar da ya kai kasar tare da wasu mutane biyu da suke yi masa rakiya, bayan da ya samu goron gayyata na musamman daga shugaban kasar ta Libya na lokacin Mu’ammar Gaddafi.
Shi ne ya kafa kungiyar "Harkatul Mahrumin" domin tallafawa marassa karfi daga cikin musulmin kasar Lebanon, bayan haka kuma yana goyon bayan gwagwarmayar da Palasdinawa suke yi da Isra’ila.
Har yanzu dai ba a san makomar Imam Musa Sadr ba, amma abin da ake da tabbaci kansa shi ne Mu’ammar Gaddafi ne ya kama shi bayan ya gayyace shi zuwa kasar ta Libya.