Mujallar Charlie Hebdo ta kasar Faransa ta sake wallafa zanen batanci ga manzon Allah, annabi Muhammad (SAW), wanda ya janyo mayakan dake ikirari da sukan jihadi suka kai mata mummunan hari a cikin shekara 2015.
Mujalar ta fitar da wannan zanen ne kwana guda kafin fara shari'ar wasu mutum 14 da ake zargi da kai hari a kan offishin mujallar dake birnin Paris,
A cewar daraktan mujallar Laurent Riss ba za su ja da baya ba, ba kuma za su karaya ba, za su ci gaba da wallafa zanen batancin ga fiyayyen halittar la’akari da cewa doka ba ta hana su aikata hakan ba.
Tuni masana suka fara danganta sake wallafa zanen da abun tsokana ga musulmi, yayin da shugaban kasar Faransa ya kare hakan da cewa dokar kasarsa bata haramta hakan ba.
Dokar Faransa dai bata hana aikata batanci ta fuskar rubuta ko furuci ko zane ga kowanne addini duk da cewa hakan cin mutunci ne mai muni ga al’ummar musulmi.
Fitar da zanen a can baya dai ya janyo tofin Allah-tsine da jerin zanga-zanga a kasashen musulmi da dama.
3920484