IQNA

22:30 - September 08, 2020
Lambar Labari: 3485161
Tehran (IQNA) Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Bayyana Cewa: Cin Zarafin Manzon Allah ( s.a.w.a) Da Jaridar Faransa Ta Yi, Manufarsa Kawar Da Hankula Daga Mikircin Amurka da Isra'ila.

Ga Cikakken Matanin Bayanin kamar Haka:

“Da Sunan Allah Ma’abocin Girma

A Wani jikon, Babban kuskuren wanda ba ya karbar yafiya da wata mujallar kasar Faransa ta yi na cin zarafin, manzo mafi girma ( s.a.w.a) ya sake bayyana boyayyar kiyayya da gabar da tsarin siyasa da al’adun yammacin turai yake da su ne akan addinin musulunci, da al’ummar musulmi.

Ko kadan ba abun yarda ba ne, jami’an kasar Faransa su fake da batun hakkin tofa albarkacin baki su ki yin tir da wannan laifi mai girma, kuma yaudarar al’umma ce.

 Siyasar adawa da gaba ta ‘Yan Sahayoniya da gwamnatoci masu girman ce tushen wannan irin kiyayya, wacce ake maimaitawa daga lokaci zuwa lokaci.

Abu ne mai yiyuwa a wannan lokacin manufarta ita ce kawar da tunanin mutane  a gwamnatoci a yammacin Asiya, daga bakaken makirce-makircen  da Amurka da ‘yan Sahayoniya su ke kitsawa wannan yankin. Ya zama wajibi ga al’ummar musulmi, musamman a yammacin Asiya, da kada su mance da kiyayyar jagorori yammacin turai da musulunci da musulmi, su kuma kasance cikin fadaka akan batutuwa masu muhimmanci da su ka shafi wannan yankin.

Allah mai yin rinjaye ne akan lamarinsa.

Sayyid Ali Khamnei

3921645

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: