IQNA

Falastinawa Za Su Yi Zanga-Zangar Allawadai Da Sarakunan Larabawa Masu Kulla Alaka Da Isra'ila

21:51 - September 14, 2020
Lambar Labari: 3485183
Tehran (IQNA) Jagororin kungiyoyin Falastinawa sun kirayi al’ummar falastinu da su fito su yi tir da Allawadai da sarakunan larabawa masu kulla hulda da gwamnatin yahudawa.

Jagororin kungiyoyin Falastinawa sun kirayi dukkanin al’ummar falastinu da su fito gobe Talata domin yin tir da Allawadai da sarakunan larabawa da suka mika wuya wajen kulla hulda da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

A cikin bayani na hadin gwiwa tsakanin shugabannin kungiyoyin Falastinawa, an kirayi dukkanin al’ummar falastinu da su fito a gobe Talata kwansu da kwarkwatarsu domin nuna rashin amincewa da shirin sarakunan larabawa na sayar da Falastinu ga yahudawan sahyuniya.

Bayanin ya ce baya ga zanga-zaga da gangami, Falastinawa su daga tutocin Falastinua dukkanin birane da kauya na Falastinu a gobe Talata, a matsayin wata alama da ke tabbatar da cewa al’ummar Falastinu ba za su taba mika wuya ga gwamnatocin larabawan masu son tabbatar da halascin mamayar Isra’ila a kan kasar Falastinu ba.

Tun a makonnin da suka gabata ne dai UAE ta sanar da kulla hulda ta diflomasiyya da gwamnatin yahudawan Isra’ila, inda a ranar Juma’a da ta gabata ma Bahrain ta bi sahun UAE wajen sanar da kulla irin wannan alaka da yahudawan., lamarin da ke ci gaba da shan kakkausar suka daga al’ummomin musulmi da na larabawa.

3922580

 

captcha