IQNA

Al'ummar Bahrain Na Nuna Rashin Amincewa Da Kulla Alaka Da Yahudawa

22:44 - September 19, 2020
Lambar Labari: 3485200
Tehran (IQNA) Al’ummar Bahrain na gudanar da jerin gwano domin nuna rashin amincewa da kulla alaka da Isra’ila da gwamnatin kasarsu ta yi.

Kwanaki biyar a jere a kowace rana al’ummar kasar Bahrain suna gudanar da jerin gwano, domin yin tir da masarautar kasar, kan mika wuya ga manufofin Amurka da na yahudawan Sahyuniya.

Masu jerin gwanon suna daga kwalaye da kyallaye da aka yi rubutu a kansu, da ke nuni da cewa kulla alaka da Isra’ila ha’inci ne da cin amanar al’ummar Falastinu marassa kariya, saboda haka ba da yawun al’ummar Bahrain gwamnatin kasar ta kulla alaka da yahudawan Isra’ila ba.

A ranar Talata da ta gabata ce dai ministocin harkokin wajen kasashen UAE da Bahrain suka nufi Amurka inda suka hadu da Trump da Netanyu, kuma suka sanya hannu a kan wasu takardu da suka kira na zaman lafiya a tsakaninsu.

3923660

 

 

 

 

captcha