Gwamnatin jihar Lagos ta bayyana cewa, majami’un kiristoci da ke jihar za su iya ci gaba da gudanar da harkokinsu na ibada, amma dole a kiyaye ka’idojin da aka gindaya, da suka hada da wanke hannuwa da fesa maganin kashe kwayoyin cuta da kuma bayar da tazara.
Dangane da gidajen silima kuwa, gwamnatin Lagos ta bayyana cewa za a iya bude kashi talatin cikin dari ne kawai.
Najeriya dai na daga cikin kasashen Afirka da suka bayyana cewa suna daukar matakan da suka dace wajen dakile yaduwar cutar, wanda hakan yasa cutar ba ta yi tasiri ba kamar wasu kasashen, duk kuwa da yawan jama’a da ke akwai a kasar.