IQNA

Sudan Ta Karyata Cewa Tana Shirin Kulla Wata Hadakar Kasuwanci Da Isra’ila

22:17 - September 24, 2020
Lambar Labari: 3485213
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Sudan ta karyata batun cewa, tana shirin kulla wata Hadaka ta kasuwanci tare da Isra’ila.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar Sudan ta ce babu gaskiya  adukkanin rahotannin da wasu kafofin yada labarai ke fada, kan cewa tana shirin kulla wata Hadaka ta kasuwanci tare da Isra’ila a yanzu.

Bayanin ya ce abin da ake yadawa ba haka yake ba, kuma babu kamshin gaskiya a cikin dukkanin wadannan rahotanni.

Tashar talabijin ta yahudawan Isra’ila I24 ta bayar da rahoton cewa,a  ranar Asabar mai zuwa za a kulla wata Hadaka ta kasuwanci da harkokin tattalin arziki tsakanin Sudan da Isra’ila.

Kasar Sudan tana shan matsin lamba daga gwamnatocin Amurka, Saudiyya da kuma hadaddiyar daular larabawa, kan ta kulla alaka da Isra’ila, amma gwamnatin kasar ta Sudan tana tana sara tana duba bakin gatari, domin ba ta san abin da hakan zai jawo mata ba a cikin kasar.

 

3925172

 

 

captcha