IQNA

23:16 - September 27, 2020
Lambar Labari: 3485221
Jami’an tsaro a kasar Bahrain sun kama wani malamin addini saboda nuna adawa da shirin gwanatin kasar na kulla hulda da sra’ila.

Rahotanni daga Bahrain sun ce a yau Lahadi jami’an tsaron kasar sun kama Shiekh Munir Ma’atuq saboda ya na yada cewa shirin kulla huldar jakadanci da Isra’ila  wanda gwamnatin kasar take yi ba ra’ayin mutanen kasar Bahrain ba ne.

Har’ila yau labarin ya kara da cewa jami’an tsaron sun kama wasu matasa guda biyu a birnin Manama babban birnin kasar da kuma yankin Siba saboda shiga cikin wata zanga-zangar yin allawadai da kulla hulda da Isra’ila wanda gwamnatin kasar ta yi.

Banda haka Jami’an tsaron sun kama Abdul-Husain Ahmad wani matashi mai tsara wakoki wanda ya tsara wake wanda a ciki yake sukar gwamnatin kasar dangane da maida hulda da Isra’ila.

A karsen watan Augustan da ya gabata ne kasashen Bahrai da hadaddiyar daular larabawa suka kulla Hulda da Isra’ila a wani bikin da aka gudanar tare da shugaban kasar Amurka a fadarsa ta white house.

 

3925587

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar bahrain ، ra’ayin mutanen kasar ، matashi ، adawa ، kulla hulda ، wakoki
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: