IQNA

19:51 - September 28, 2020
Lambar Labari: 3485227

Zarif Ya Tattauna Da Ministocin Harkokin Wajen Azerbaijan Da Armenia Domin Sulhunta Su

Tehran (IQNA) Iran ta sanar da cewa tana kokarin shiga tsakanin kasashen Azarbaijan da kuma Armenia domin sasanta su kan rikicin da suke yi.

Zarif Ya Tattauna Da Ministocin Harkokin Wajen Azerbaijan Da Armenia Domin Sulhunta Su

A cikin wani bayani da ya fito daga ma’aikatar harkokin wajen Iran, an bayyana cewa a kokarin da kasar take yi domin sasanta kasashen Azarbaijan da kuma Armenia a rikicin da ya kunno kai a tsakaninsu,a  daren jiya Litinin, ministan harkokin wajen Iran ya zanta da jami’an gwamnatocin kasashen biyu.

Muhammad Jawad Zarif ya zanta ministocin harkokin wajen kasashen Azarbaijan da kuma Armenia a lokuta daban-daban a daren jiya, inda yake kokarin ganin an samu sulhu da fahimtar juna, domin kawo karshen tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin kasashensu.

Iran ta bayyana kasashen biyu a matsyin makwabtanta, wadanda zaman lafiyarsu zaman lafiyarta ne, a kan haka za ta ci gaba da yin kokari domin sulhunta su.

 

3925813

 

captcha