Kakakin ma’ikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatibzadeh ya bayyana cewa, zargin da mahukuntan Saudiyya suka yi ba sabon lamari ba ne, maimaici ne, kuma zai fi kyau ga mahukunatn na masarautar Al Saud da su zabi hanyar bin gaskiya da yin amfani da hikima domin kare mutuncinsu.
Ya ce ko lokutan baya sun zargi wasu da suka danganta su da ayyukan ta’addanci saboda ra’ayoyinsu an siyasa, ko kuma saboda banbancin akida, wanda hakan ba daidai ba ne.
Khatibzadeh ya ce a kokarin da mahukuntan Saudiyya suke yi domin neman burge iyayen gidansu, suna kirkirar karya tare da danganta ta da kasar Iran, kuma su cutar da mutanen kasarsu da ke adawa ta siyasa a kan tsarin kama karya na kasar, ta hanyar danganta su da ayyukan ta’addanci.
Ya ce irin wadannan makirce-makirce ba za su iya cutar da Iran ba, domin kuwa ta saba da su tsawon shekaru daga iyayen gidan sarakunan Saudiyya.
Bayanin nasa ya kara da cewa, a duniya kowa ya san inda cibiyar akidar ta'addanci da sunan addini take, inda kungiyoyin 'yan ta'adda na alqaeda da IS da makamantansu suke samo tunanin tsatsauran ra'ayi na ta'adanci, da kafirta musulmi.
3926193