IQNA

Allah Ya Yi Wa Sarkin Kasar Kuwait Rasuwa A Yau

23:25 - September 29, 2020
Lambar Labari: 3485230
Tehran (IQNA) Gwamnatin kasar Kuwait ta sanar da mutuwar sarkin kasar a yau bayan fama da rashin lafiya.

Majiyar fadar sarkin kuwait ta bada sanarwan cewa Sarki Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-Jabir Assabah ya rasu yana dan kimanin shekaru 91 a duniya.

Rahotanni daga kasar ta Kuwait sun bayyana cewa sarkin ya dan dade yana fama da rashin lafiya. Har yanzun dai ana jiran Karin bayani dangane da rasuwar sarkin.

Har’ila yau a wani Labarin kuma gwamnatin kasar Kuwait ta ki amincewa da shugabancin kungiyar kasashen Larabawa karo na dari da biyar bayan da gwamnatin Falasdinawa a Ramallah ta ki amincewa da shugabancin.

Kafin haka dai a ranar Talatan da ta gabata ce gwamnatin Falasdinawa a Ramallah ta ki amincewa da karbi shugabancin karba-karba na kungiyar kasashen Larabawan, saboda maida huldar jakadancin da kasashen Bahrai da Hadaddiyar daular larabawa suka yi da kuma goyon bayan da kungiyar ta nuna dangane da hakan.

A ranar sha biyar ga watan Satumban da muke ciki ne kasashen biyu suka rattaba hannun kan yarejejeniyar maida huldar jakadanci da Isra’ila a fadar shugaban kasar Amurka.

 

3926288

 

captcha