Muhawarar wadda aka tafka tsawon mintuna casa'in wadda kuma aka watsa kai tsaye a kafofin yada labarai na Amurka da ma na duniya, ta nuna yadda mutanen biyu suka yi ta sukar junansu da kuma fallasa kansu.
A bisa ga yadda muhawarar ta gudana, Trump ya kasance a mai kare kansa ne bisa tuhumce-tuhumce a mafi yawan lokacin muhawarar, yayin da shi kuma Biden ya kasance mai kai farmaki a kan Trump.
Wasu sun yi la'akari da cewa a cikin kalamansa Joe Biden ya yi amfani da kalmar "Insha'allah" wato kalmar ad musulmi suke fadia cikin zantukansu.
Biden ya bayyana Trump a matsayin wanda ya kara ruruta wutar rikicin wariyar launin fata da ake nuna ma bakaken fata akasar Amurka, inda Trump ya rika sukar masu zanga-zanga tare da kiransu a matsayin ‘yan daba ‘yan ta’adda, yayin da shi kuma Trump ya kare kansa da cewa, zanga-zangar ba ta zaman lafiya ba ce.
3926400