IQNA

23:43 - October 11, 2020
Lambar Labari: 3485264
Tehran (IQNA) Magajiyar gari bakar fata musulma ta farko a kasar Burtaniya ta yi murabus daga jam’iyar Labour saboda nuna mata wariya.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, Raqiya Islam’il magajiyar gari bakar fata musulma ta farko a kasar Burtaniya ta yi murabus daga jam’iyar Labour saboda nuna mata wariya da ake yi a jam’iyyar, saboda ita bakar fata ce.

Raqiya Isma’ila wadda ‘yar asalin kasar Somalia ce, ta zama magajiyar gari a Islington da ke cikin gundumar London a kasar Burtaniya tun a cikin shekarar da ta gabata.

Ta ce ta yi la’akari da cewa ana nuna mata banbanci matuka saboda dalilai guda biyu, na daya dai ita musulma ce, na biyu kuma ita bakar fata ce, wanda hakan yasa ba ta samun damar yin harkokinta a cikin jam’iyyarta ta Labour kamar yadda sauran ‘yan jam’iyyar fararen fata suke da damar yin hakan.

Ta ce sau tari ta kan yi niyar gudanar da wasu taruka na addinin musulunci amma ba a bata damar yin hakan, kamar hatta a tarukan jam’iyyar, idan tana magana sai wasu su ce da ita ta rufe bakinta, wanda hakan yasa ta yanke shawarar barin jam’iyyar.

Tun daga lokacin da Keir Starer ya zama shugaban jam’iyyar Labour a cikin watan Afirilun da ya gabata, nuna wariya ga bakaken fata da musulmi ya karu a cikin jam’iyyar Labour.

 

3928680

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: