IQNA

Iran Ta Ce Tana Fatan Ganin Iraki Ta Dawo Da Karfinta

23:41 - October 28, 2020
Lambar Labari: 3485315
Sakataren majalisar fayyace maslahar tsarin musulunci a Iran ya bayyana cewa Iran fatan ganin Iraki ta dawo da karfinta a yankin.

Sakataren majalisar fayyace maslahar tsarin musulunci a kasar Iran, ya bayyana cewa yana cikin siyasar kasar ganin cewa kasar Iraki ta zama ‘yantacciya mai karfi sannan da hadin kai.

Mohsen Rizaei ya bayyana haka a yau Laraba a lokacin da yake ganawa da shugaban rundunonin masu gwagwarmaya a kasar Iraki, wadanda ake kira Hashdu, Sheikh Akbar Alkaabi a nan birnin Tehran.

Muhsen Rizaei ya kara da cewa, gwamnatin kasar Amurka ta na son kasashen larabawa makha’inta su fuskanci kawancen masu gwagwarmaya a yankin, amma Amurka ba ta da zabi in banda ficewa daga yankin.

Har’ila yau Amurka tana son maida Isra’ila a matsayin wakilinta a yankin Asia ta kudu wanda hakan ma ba zai yu ba.

Rizae ya kammala da cewa kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar Iraqi su na kara karfi duk tare da matsalolin da kasar Amurka take haddasa su a kasar.

A na shi bangaren Sheikh Kaabi ya bayyana cewa Amurka ta na kokarin ganin ta haddasa yakin cikin gida a kasar Iraki wanda zai ba ta damar rarraba kasar nan gana.

Shugaban dakarun Nujabaa ya kammala da cewa ofishin jakadancin Amurka a Bagdaza cibiyar yada fitina a kasar Iraki kawai.

3931920

 

captcha