IQNA

22:21 - November 03, 2020
Lambar Labari: 3485333
Tehran (IQNA) yahudawan sahyuniya sun rusa gidaje 11 mallakin Falastinawa.

Kamfanin dillancin labaran anatoli ya bayar da rahoton cewa, Mu’utaz Bashara daya daga cikin jami’an yankin Agwar da ke arewacin yankin kogin Jordan, ya bayyana cewa yahudawan Isra’ila sun kaddamar da farmaki a yankin, inda suka rusa gidaje 11 dukkaninsu mallakin Falastinawa.

Jami’an yahudawan sun fake da hujar cewa gidajen ba a gina su da inganci ba, ko kuma hujjar cewa Isra’ila bata bayar da izinin gina su tun daga farko ba.

Bisa rahotannin da hukumomin Falastinawa suka, daga farkon wannan shekara da muke ya zuwa yanzu, Isra’ila ta rusa cibiyoyi da gidaje fiye 500 dukkaninsu mallakin Falastinawa, bisa hujjoji daban-daban, domin samun damar gina matsugunnan yahuwada ‘yan share wuri zauna a cikin wadannan yankuna na Falastinawa.

 

3933101

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: