IQNA

23:35 - November 20, 2020
Lambar Labari: 3485383
Tehran (IQNA) daruruwan jami’an ‘yan sanadan gamnatin yahudawan Isra’ila sun hana musulmi gudanar da sallar Juma’a a cikin masalacin Quds.

Shafin jaridar Daily Sabah ya bayar da rahoton cewa, jami’an tsaron yahudawan Isra’ila dauke da muggan makamai sun tare hanyoyin isa masallacin aqsa domin hana musulmi gudanar da sallar Juma’a.

Dukkanin Falastinawan da suke shigowa cikin birnin quds daga yankunan falastinawa da ke Nablus da yammacin kogin Jodan, yahudawa sun hana su isa masallacin aqsa domin halartar sallar Juma’a.

Limamin masallacin qasa Sheikh Yusuf Sininah ya bayyana cewa, makonni hudu kenan a jere, gwamnatin Isra’ila tana hana musulmi shigowa cikin birnin quds domin yin sallar Juma’a.

Ya ce wannan daya ne daga cikin irin matakan da gwamnatin Isra’ila ake dauka wajen take hakkokin musulmi na Falastinu wadanda ta mamaye musu kasa.

 

3936308

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: