IQNA

Dakarun Yemen Kai Hain Mayar Da Martani A Kan Saudiyya

22:28 - November 23, 2020
Lambar Labari: 3485392
Tehran (IQNA) sojojin Yemen tare da dakarun sa kai na kabilun larabawan kasar sun harba makamai masu linzami a kan kamfanin mai na Aramco a jusa da birnin Jiddah.

Kafofin yada labarai a birnin San’a ta bayar da rahoton cewa, kakakin rundunar sojin kasar Yemen Brig Gen. Yahya Sari ya fadi a safiyar yau cewa, a wani mataki na mayar da martani kan kisan kiyashin da masautar Al Saud take yia kan al’ummar kasar Yemen, da jijjifin safiyar yau Litinin, sun harba makami mai linzami samfurin quds-2 a kan wata cibiya ta kamfanin mai na Aramco.

Ya ce wannan mataki da ke zuwa a matsayin martani da ramuwar gayya, wanda yake zuwa a daidai lokacin da masarautar iyalan gidan Saud ke ta kara zafafa hare-harenta a kan al’ummar kasar yemen, tare da kashe mata da kananan yara da tsoffi.

Brig Gen. Yahya Sari ya ce; muna kiran mutanen gari fararen hula gami da ma’aikatan kamfanoni na kasashen ketare das u akuracewa wadannan muhimman wurare, domin kuwa suna daga cikin wuraren da hare-haren mayar da martanin al’ummar kasar Yemen kan mahukuntan Saudiyya zai shafa.

Mahukuntan masarautar ta Al Saud dai sun ki cewa komai akan wannan batu duk kuwa da cewa wasu kafofin yada labarai na kawayensu daga cikin turawa sun tabbatar da labarin.

3936809

 

captcha