IQNA

Fitaccen Mai Wasan Barkwanci Na Amurka Ya Bayyana Abin Da Ya Ja Hankalinsa Har Ya Musulunta

23:21 - November 24, 2020
Lambar Labari: 3485397
Tehran (IQNA) fitaccen mai wasan barkwanci dan kasar Amurka David Chappelle ya bayyana yadda ya karbi addinin muslunci.

Shafin National ya bayar da rahoton cewa, David Chappelle ya bayyana yadda ya muslunta a wata zantawa da ya yi da wata tashar talabijin ta kasar Amurka, inda ya bayyana kyakkayawar mu’amala da musulmi suke yi masa ne ya yi tasiri a kansa.

A lokacin da mai gabatar da shirin na talabijin ya tambaye kan dalilan da suka sanya ya muslunta, ya bayyana cewa maganar gaskiya ita ce saboda kyakkayawar mu’amala ta musulmi a Amurka.

Ya ce a lokacin da bai wuce shekaru 17 da hahuwa ba, wato shekaru talatin da suka gabata, yakan je wani shago na musulmi a cikin birnin Washington inda yakan yi sayayya, kuma musulmin da suke wurin suna kyautata masa matuka.

Ya kara da cewa, sakamkon yadda musulmin nan suke mu’aala da shi duk da cewa sun san shi kirista ne, da kuma yadda suke kyautata masa, da kallonsa tamkar dan uwansu na jinni, hakan ya yi tasiri a zuciyarsa, inda daga karshe ya gane cewa abin da suke yi koyarwa ce irin ta addininsu, wato addinin muslunci.

David Chappelle ya je aikin hajji, kuma ya hadu da musulmi daga kasashen duniya, inda ya kara samun masaniya dangane da addinin muslunci, duk da cewa yana da karbuwa a wajen Amurka saboda wasan barkwanci, amma duk da haka yana riko da addinin muslunci a rayuwarsa yadda ya kamata.

3936795

 

captcha