IQNA

An Saki Mahir Akhras Daga Gidan Kason Isra’ila

23:31 - November 27, 2020
Lambar Labari: 3485407
Tehran (IQNA) yahudawa sun saki Mahir Akhras wanda ya kwashe tsawon kwanaki fiye da dari yana yajin cin abinci.

Shi dai Mahir Akhras wanda ‘yan sahoniya suke tsare da shi ya yi yajin cin abinci na fiye da kwanani 100 a gidan kurkuku, da a karshe ya tilastawa ‘yan sahayoniyar sakinsa.

Tun da fari, ‘yan sahayoniyar sun kama shi ne ba tare da wani dalili ba, sannan kuma aka tsare shi ba tare da an yi masa sharia ba.

A cikin wani bayani da kakanin kungiyar Hamas, Hazim Kassim ya fitar ya bayyana cewa; Muna yi wa Mahir Akhras murnar samun ‘yancin da ya yi daga kurkukun ‘yan sahayoni, wanda hakan yake nuni da juriyar palasdinawa da jajurcewarsu har zuwa ga samun nasara.

Ita ma kungiyar Jihadul-Islami ta bayyana cewa; Gwagwarmayar da Akharas ya yi ta hanyar yajin cin abinci, kwakkwaran dalili ne akan cewa al’ummar Palasdinu ba ta karbar kasakanci ko kadan.

Wasu kungiyoyin na Palasdinawa da dama sun fitar da bayanai da su ke yin jinjina ga Mahir Akhras akan tsayin dakar tashi da kuma jajurcewa.

 

3937521

 

captcha