IQNA

Wani Dan Kasar Korea Ta Kudu Da Ya Musulunta Yana Sauraren Karatun Kur’ani Mai Tsarki

22:53 - December 02, 2020
Lambar Labari: 3485421
Tehran (IQNA) wani dan kasar Korea ta kudu da ya musulunta yana sauraren karatun kur’ani mai tsarki.

Wani dan kasar Korea ta kudu da ya musulunta bad a jimawa ba yana sauraren karatun kur’ani mai tsarki daga bakin Yahya Sidqi da kasar Morocco, inda ya nuna mamaki da jin kur’ani, wanda hakan ke tabbatar da cewa wannan ba zancen mutum ba ne.

Ya ce bayan musuluntarsa yana sauraren wasu ayoyin kur’ani a cikin wayarsa, amma  awannan karon ne yake sauraren karatu na kur’ani a cikin tilawa da irin wannan salo.

Ya ce hakika sauraren wannan karatu ya kara masa imani da Allah madaukakin sarki, tare da tabbatar da cewa kur’ani zance ne na Allah ba ba na dan adam ba.

3938678

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar Korea ta kudu
captcha