IQNA

Iran Ta Ce Jami’an Tsaronta Sun Gano Wasu Masu Hannu A Kisan Babban Masanin Nukiliya

22:29 - December 04, 2020
Lambar Labari: 3485427
Tehran (IQNA) Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta bayyana gano wasu mutane dake da hannu a kisan masanin nukiliyarta, Mohsen Fakhrizadeh.

Da yake sanar da hakan, kakakin ma’aikatar leken asirin kasar ta Iran, ya ce an gano mutanen dake da hannu a kisan masanin nukiliyar, wadanda suka shigo da wasu kayayaki da na’urori da akayi amfani dasu wajen aiwatar da kisan a cikin kasar.

Ali Rabiei, ya ce dama majalisar koli ta tsaron kasar ta fitar da irin wadannan bayannan.

Koda yake labarin bai bayyana mutum nawa ne, amma ya ce, daga cikin mutanen akwai wadanda suka shigo da wasu na’urorin da kuma wadanda sukayi aiki da fasahohi.

A ranar Juma’a data gabata ne masanin nukiliyar kasar ta Iran, Mohsen Fakhrizadeh, ya yi shahada a wani hari da aka kai masa a wajen birnin Tehran, wanda mahukuntan kasar ta Iran suka dora alhakin hakan ga makiyyan kasar a sahun gaba Isra’ila, tare da sha alwashin maida martani a lokacin da ya dace.

 

 

3938811

 

 

 

 

captcha