IQNA

Saudiyya Ta Ce Yin Sulhu Da Isra’ila Na Da Muhimmanci

19:15 - December 05, 2020
Lambar Labari: 3485432
Tehran (IQNA) ministan harkokin wajen kasar Saudiyya ya bayyana cewa, yin sulhu da Isra’ila yana da muhimmanci matuka.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Faisal Bin Farhan Bin Abdullah ya bayyana cewa, yin sulhu da gwamnatin yahudawan Isra’ila yana da muhimmanci domin samun zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Ministan na masarautar Saudiyya ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ta gudana tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen yankin tekun Mediterranean kan batutuwa na tsaro.

Haka nan kuma ya yi da’awar cewa kulla alaka da gwamnatin Isra’ila da wasu kasashen larabawa suka yi ne ya dakatar da shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa na yammacin kogin Jordan.

Wannan furuci na ministan Saudiyya na zuwa a daidai lokacin da shi kuma anasa bangaren firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu yake jaddada cewa; kulla alaka da gwamnatocin larabawa ba zai dakatar da shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan ba.

3939083

 

 

 

captcha