Tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, a ganawar da ta gunada tsakanin shugaban Masar Abdulfattah Al-sisi da kuma shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a ziyarar da ya kai a kasar, ya sheda wa Macron cewa, kada su fake da sunan ‘yancin fadar albarkacin baki, suna bakantawa daruruwan miliyoyi.
Al – sisi ya ce da Macron, addini da akida da sauran abubuwa da suke da alaka da ubangiji, abubuwa ne da suke birbishin kowane dan adam komai matsayinsa, domin mutane su ne baiwa dan adam wani matsayi na duniya, amma matsayi wanda Allah ne ya daukaka annabawa da shi, babu wani mahaluki da zai iya kai wa ga wannan matsayin balanta ya yi cin zarafi ko tozarci a kansa da sunan ‘yancin fadar albarkacin baki.
A nasa bangaren shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya mayar da nasa bayanin da cewa, abin da musulmi suke magana a kansa na zanen batunci ga ma’aiki ba gwamnatin Faransa ce ta yi hakan ba, wata jarida ce mai zaman kanta, saboda lamarin ba shi da wata alaka da gwamnatin Faransa.
Tun bayan nuna zanen batuncin da aka yi a kan Faransa a baya-bayan nan a kan ma’aiki (SAW) Macron ya fito ya kare masu yin zanen, tare da bayyana cewa suna damar yin hakan kamar yadda dokar kundin tsarin mulkin Faransa ta yarje musu.
3939721