A raton da tashar TRT ta bayar ta bayyana cewa, tun a ranar 2 ga watan Oktoban da ya gabata ne shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya gabatar da daftarin doka ga majalisar ministocin kasar, da ke nufin daukar tsauraran matakai a kan musulmi, domin yaki da abin da ya kira tsatsauran ra’ayi.
A zantawarsa da manema labarai a jiya, firayi miistan kasar Faransa Jean-Castex ya sheda wa manema labarai cewa, majalisar ministocin kasar Faransa ta amince da wannan daftarin doka, inda a halin yanzu za a ci gaba da yin aiki da ita a fadin kasar.
Ya ce wannan dokar ba ta nufin takurawa musulmi ko cin zarafinsu, manufar dokar ita ce yaki da masu tsatsauran ra’ayi daga cikin musulmi, domin kare kasar Faransa da al’adunta da kuma abubuwan da ta gada a tarihinta, tare da tabbatar da cewa ba su gurbata ba.
Sai dai a daya bangaren wannan batu na ci gaba da shan kaakusar suka da kuma mayar da martani daga al’ummomin duniya musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, da kuma kungiyoyin kare hakkokin bil adama na duniya, gami da jam’iyyun siyasa masu adawa a cikin kasar ta Faransa.
Ita ma a nata bangaren shugabar kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya Michel Bachelet ta bayyana cewa, wannan dokar za ta takura musulmi da sanya ido a kansu da masallatansu, kamar yadda kuma za ta karfafa nuna wariya tsakanin al’ummomi a kasar Faransa, musamman ma wadanda su ne marassa rinjaye, wanda hakan take hakkokinsu ne, kuma ya sabawa doka ta duniya.
Musulmin kasar Faransa wadanda adadinsu ya haura miliyan biyar, su ne na biyu wajen yawa a kasar bayan mabiya addinin kirista.