Shafin yada labarai na Al-sabq na kasar saudiyya ya bayar da rahoton cewa, Sheikh Abdullatif minista mai kula da harkokin addini kuma mai sanya ido a kan ayyukan buga kur’ani mai tsarki a madaba’antar sarki Fahad ya bayyana cewa, daga shekara ta 1405 da aka kafa wanann madabanta ya zuwa yanzu, an buga kur’anai miliyan 342 a cikin harsuna 78 na duniya.
Ya ci gaba da cewa bisa la’akari da ci gaba da ake samu a kowane lokacia duniya, ya zamaita ma wanann madaba’anta ta kara himma wajen samar da abubuwa da za su zama masu amfani ga musulmi a duniya, wadanda za su rika tafiya tare da zamani.
Ya ce baya ga manhajoji daban-daban da aka samar wadanda ake yin amfani da tahnayoyin wayar salula, da suka shafi sha’anin kur’ani da karatu da ma harda, a halin yanzu kuma ana kara kirkiro wasua bubuwa na daban.
Babban abin da aka samar a wannan lokaci a wannan madaba’nata shi ne wani tabarau da yake yin aiki da manhaja ta musamman, domin bayyana yadda masallacin manzon Allah yake, da abubuwan da ya kunsa da yakunsa kuma yin bayani kansu dalla-dalla.
Daga ciki hard a nuna wurare da kuma yadda suke a da a cikin tarihin addinin muslunci, domin mutane su sam matsayin wurare daban-daban da sukea cikin masallacin ma’aiki da kewaye.
Wasu daga cikin abubuwan da wannan tabarau yake nunawa har da Raudah, da kuma matsayinta a cikin addini tun daga lokacin manzon Allah (SAW) da kuma falalarta.
Gwamnatin kasar Saudiyya a halin yanzu tana son jawo masu ziyara da bude ido domin ganin da kuma sanin muhimman abubuwa na tarihi da suke a kasar musamamn wadanda suka shafi addinin muslunci, wanda a lokutan baya take rusa su, da ma batar da su, tare da hana masu ziyara isa irin wadannan wurare masu daraja albarka.