
Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, wata cibiyar bayar da taimako a kasar Turkiya mai suna Khairat, ta bayar da taimako na kwafin kur'ani guda dubu 30 a kasar Jibouti.
An tura dukkanin kwafi-kwafin na kur'ani mai tsarki daga Turkiya zuwa kasar Jibouti da ke gabashin nahiyar Afirka.
Ali Usman Islahanchi wakilin cibiyar ya sheda wa manema labarai cewa, cibiyar tana gudanar da irin wadannan ayyuka na raba kayan taimako daban-daban.
Ya ce a halin yanzu cibiyar ta raba kur'anai masu tarin a cikin nahiyar Afirka, kamar yadda kuma ta raba wasu a cikin gida, inda ya zuwa yanzu adadin kwafin kur'ani da ta raba ya kai dubu 600.