
Tashar talabijin Russia Today ta bayar da labarin da yake cewa; Baitul-malin kasar Amurka aa sanar da saka kungiyar Sarayal-Mukhtar ta kasar Bahrain a cikin kungiyoyin da take kira na 'yan ta'adda tare da kakaba mata takunkumi.
Rahoton Baitul-malin kasar Amurkan ya bayyana kungiyar a matsayin barazanar tsaron kasar, tare da bayyana matakin da cewa sako ne mai karfi zuwa ga Iran.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pempeo ya riya cewa kasar tasa ba za ta bari kungiyoyi masu alaka da Iran su ci gaba da zama barazana ga Amurkan ba.
Tuna cikin shekara ta 2011 ce dai al'ummar Bahrain suka fara bore domin neman 'yanci an siyasa da kuam neman fita daga karkashin mulkin mulukiya da kama karya na sarakuna, inda suka bukaci sarki ya ci gaba da mulkinsa, amma al'ummar kasa su rikazaben 'yan majalisa da kansu wadanda za su zabi firayi minista.
Amma masarautar kasar ta yi amfani da karfi wajen murkushe jama'ar kasar tare da taimakon Amurka da Burtaniya gami da Saudiyya da kuma Isra'ila.
3941368