IQNA

‘Yan Gwagwarmaya A Iraki Sun Soki Amurka Kan Yin Afuwa Ga Amurkawan Da Suka kashe Irakawa

22:55 - December 24, 2020
Lambar Labari: 3485489
Tehran (IQNA) kungiyoyin gwagwarmayar Iraki sun yi kakakusar suka kan Amurka dangane da afuwar da ta yi wa Amurkawa da suka yi Irakawa kisan gilla.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, kungiyar Hizbullah a Iraki da sauran kungiyoyin gwagwarmayar kasar sun yi kakakusar suka kan Amurka dangane da afuwar da ta yi wa Amurkawa da suka yi Irakawa kisan gilla a lokacin da suka mamaye kasar.

Ita ma a nata bangaren Majalisar Dinkin Duniya ta caccaki shugaban Amurka Donald Trump kan yafe wa ma'aikatan kamfanin tsaro na Black Water da aka same su da laifukan cin zarafi da kisan fararen hula a kasar Iraki.

Kakakin kwamitin kare hakkin bil adama a majlaisar dinkin duniya Marta Hurtado ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da matakin da bayyana matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na yafe wa Amurkawa ma’aikatan kamfanin tsaro na Black Water da suka yi kisan gilla  akan fararen hula a Iraki.

Marta Hurtado ta ce abin da Trump ya yi  yana a matsayin karfafa gwiwar masu aikata irin wadannan laifuka, tare da basu tabbacin cewa za su kubuta daga shari’a, wanda kuma hakan yana  a mtsayin keta hurumi ne na doka, kasantuwar cewa mutanen duk an yanke musu hukunci bisa ga munanan laifukan da suka aikata na kisan gilla a kan faraen hula a Iraki.

 

3943053

 

captcha