IQNA

23:32 - December 25, 2020
Lambar Labari: 3485490
Tehran (IQNA) shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya aike da sakon taya murna ga shugabannin kasashe daban-daban kan zagayowar lokain haihuwar annabi Isa (AS).

A cikin sakon nasa, shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya bayyana cewa, duniya a halin yanzu tana bukatar yin aiki na hadin gwiwa tsakanin dukkanin al’ummomi na duniya, domin tunkarar abubuwan da suke a matsayin kalubale ga ‘yan adam baki daya, inda a halin yanzu daya daga cikin misalin hakan shi ne yaki da cutar corona.

Haka nan kuma shugaba Rauhani ya yi ishara da cewa, annabi Isa (AS) manzo ne daga cikin manzannin Allah, wanda ya yada sulhu da da kaunar juna a tsakanin bil adama, wanda kuma wannan shi ne tafarki na dukkanin annabawan Allah amincin Allah ya tabbata gare su, wato kira zuwa ga tsira wanda hakan yana kunshe a cikin bin tafarkin ubangiji da kiyaye dokokinsa.

Ya yi fatan alhairi ga takwarorinsa na duniya, tare da yin fatan wannan shekara ta miladiyya mai kamawa ta zo ma al’ummomin duniya da alhairi da albarka da yalwatar arziki da zaman lafiya.

3943155

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: