IQNA

Nasrallah: Amurka Da Isra’ila Da Saudiyya Ne Suka Kashe Qassem Sulaimani

21:39 - December 28, 2020
Lambar Labari: 3485501
Tehran (IQNA) babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, gwamnatocin Amurka, Isra’ila da Saudiyya ne suka kashe Qassem Sulaimani da Abu Mahdi Almuhandis.

A wata zantawa da ya yi da tashar talabijin ta Almayadeen a daren jiya, dangane da cikar shekara guda da kisan babban kwamandan sojin Iran Qassem Sulaimani da abokinsa kuma mataimakin kwamandan dakarun Hashd Sha’abi Abu Mahdi Almuhandis, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya tabo batutuwa da dama da suka shafi wannan batu, da ma wasu batutuwan da suka shafi siyasar yankin gabas ta tsakiya.

Da farko dai ya fara ne da bayyana irin gagarumar gudunmawar da Qassem Sulaimani ya bayar wajen tunkarar shirin Amurka da Isra’ila ‘yan korensu wajen rusa wasu kasashen musulmi da na larabawa a yankin gabas ta tsakiya, musamman a kasashen Lebanon, Syria, Iraki da kuma Falastinu.

Nasrullah ya ce Qassem Sulaimani ya bayar da gudunmawa babba wajen fatattakar Isra’ila a lokacin da ta kaddamar da yaki kan kasar Lebanon a shekara ta 2006, kamar yadda kuma dama tun tsawon shekaru shi ne gishikin taimakawa kungiyoyin Falastinawa wajen tunkarar Isra’ila musamman a Zirin Gaza, kamar yadda kuma ya gudunmawar da ya bayar a Syria da Iraki wajen yaki da ‘yan ta’addan Daesh ba a boye take ga kowa a duniya ba.

Dangane da wata tafiya da Qassem Sulaimani ya yi zuwa kasar Rasha a shekarun baya kuwa, Nasrullah ya bayyana cewa, Qassem Sulaimani ya gana da shugaba Putin tsawon sa’oi biyua  jere, inda ya gamasar da Putin kan muhimmancin shigar Rasha a cikin yakin da manyan kasashen duniya da wasu gwamnatocin larabawa suka kaddamar a kan Syria da nufin rusa ta, inda sakamakon haka ne Rasha ta tura sojoji mayaka domin yaki da ‘yan ta’adda da kasashen duniya ke amfani da domin rusa kasar Syria.

Ya ce tun kafin wannan lokacin Amurka da Isra’ila da wasu ‘yan korensu a cikin kasashen larabawa suna da shirin yin kisan gilla a kan Qassem Sulaimani, amma ba su samu sa’ar hakan ba saia  shekarar da ta gabata, kasantuwar ya zama babban karfe kafa da ke kawo cikas ga manufofin Amurka da Isra’ila a yankin gabas ta tsakiya.

A wani bangaren kuma Sayyid Nasrullah ya yi ishara da yadda gwamnatin Saudiyya ta roki gwamnatin Trump da shi a kasashe shit un kafin kisan Qassem Sulaimani, inda yarima Saudiyya Muhammad Bin Salman da kansa ne ya nemi wannan alfarma daga Donald Trump a ziyararsa ta farko da ya kai Amurka a fadar White House, amma Amurka ta nuna masa hadarin da ke tattare da hakan, sai Bin Salman ya dage kan cewa za su biya kudi ko nawa ake bukata domin tunkarar abin zai biyo bayan kashe Nasrullah.

Dangane da yadda gwamnatocin kasashen larabawa suke ta hankoron ganin sun kulla alaka da Is’ila tare da yin watsi da al’ummar falastinu kuwa, ya bayyana manufar hakan da cewa ita ce hada babban kawance tsakanin larabawa da yahudawan Isra’ila wajen tunkarar Iran, kamar yadda Amurka da Isra’ila da kuma wasu daga cikin gwamnatocin larabawa suka fadi hakan da kansu.

Dangane da halin da kungiyar Hizbullah take a halin yanzu kuwa, Nasrullah ya bayyana cewa, karfin kungiyar ya karu fiye da kowane lokaci a  cikin tarihinta, inda daga shekarar da ta gabata zuwa wanannshekara karfin ya ninka sau biyu, kuma ya bayar da tabbacin cewa a halin yanzu kungiyar tana da makamai masu linzami da ba su kure wajen samun abin da aka saita su a kanta.

Sayyid nasrullah ya ce, a halin yanzu kungiyar Hizbullah za ta iya kai hari kan dukkanin abin da take bukata a cikin Isra’ila ba tare da kure ba, kuma a duk lokacin da Isra’ila ta yi gigin sake kaddamar da wasu hare-hare a kan kasar Lebanon, to ta kwana da sanin cewa ba za ta iya jurewa martanin kungiyar Hizbullah ba.

3943772

 

captcha