IQNA

Desmond Tutu: Dole Ne Amurka Ta Kawo Karshen Taimakonta Ga Isra’ila

23:20 - January 03, 2021
Lambar Labari: 3485519
Tehran (IQNA) Tsohon shugaban majami’ar kiristoci a kasar Afirka ta kudu Desmond Tutu, ya bukaci sabuwar gwamnatin Amurka da ta kawo karshen mara baya ido rufe da Amurka ke yi ga Isra’ila.

A cikin wata makamalarsa da jaridar Guardian ta kasar Burtaniya ta buga, Desmond Tutu ya bayyana cewa, Amurka tana mara baya ga Isra’ila tare da ba ta kariya wajen ci gaba da mallakar makaman nukiliya, wanda hakan baya ga kasancewarsa babban hadari ga duniya, a lokaci guda kuma ya yi hannun riga da dokoki na kasa da kasa.

Tutu ya ce sakamakon goyon bayan da Isra’ila take samu ne ido rufe daga Amurka take danne hakkokin Falastinawa tare da gallaza musu, ba tare da wani ya iya taka mata burki ba kan hakan.

Ya ce mutane da dama suna fata kan gwamnatin Biden, domin ganin ta kamanta yin abin da ya dace, domin dawo da mutuncin Amurka da ya riga ya zube a idon duniya, wanda kuma hakan ba zai yiwuwa ba, har sai gwamnatin Amurka ta mutunta dokokin duniya, tare da kare hakkokin ‘yan adam, da kuma taka wa Isra’ila burki kan laifukan da take tafkawa.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, mallakar makaman nukiliya ba abu ne da ya dace da zaman lafiyar duniya ba, amma kuma bai kamata wasu su zama ‘yan lele dangane da wannan batu mai matukar hadari ga makomar zaman lafiyar duniya ba, domin kuwa rashin sanya ido kan makaman nukiliya na Isra’ila, yana daya daga cikin manyan hadarori da duniya ke fuskanta.

3945019

 

captcha