IQNA

An Kafa Wani Mutum-Mutumin Qassem Sulaimani A Birnin Beirut Na Kasar Lebanon

14:43 - January 06, 2021
Lambar Labari: 3485530
Tehran (IQNA) an kafa wani Mutum-Mutumin Qassem Sulaimani a cikin birnin Beirut na kasar Lebanon.

Rashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a jiya an kafa wani Mutum-Mutumin Qassem Sulaimani a cikin birnin Beirut na kasar Lebanon, domin girmama shi da kuma jan aikin da ya yi wa al'ummar kasar wajen taya su yaki da Isra'ila har zuwa lokacin korarta daga kasar.

Taron kafa wannan mutum-mutumin dai ya samu halartar wasu jami'an gwamnati gam,mi da wasu masana da kuma wakilan kungiyoyi na kasar ta Lebanon, da kuma wakilan kungiyoyin Falastinawa mazauna kasar Lebanon.

An kafa wannan mutum-mutumi ne a yankin Gabiri da ke cikin birnin Beirut, inda magajin garin yankin ya jagoranci kafa wannan mutum-mutumi domin tunawa da Kasim Sulaimani.

Kafin wannan lokacin ma an kafa wani makamancinsa a yankin Marus Ra'as da ke kudancin kasar ta Lebanon.

 
رونمایی از تندیس سردار سلیمانی در پایتخت لبنان + فیلم / اماده
رونمایی از تندیس سردار سلیمانی در پایتخت لبنان + فیلم / اماده

3945994

 

captcha