IQNA

22:47 - January 11, 2021
Lambar Labari: 3485544
Tehran (IQNA) an gudanar da wani taro ta hanyar yanar gizo day a hada malamai dam asana daga kasashen duniya dangane da cikar shekaru shida da kisan Sheikh Baqir Nimr.

Taron wanda ya gudana ta hanyar hotunan bidiyo na yanar gizo, ya samu halartar malaman addini da kuma masana da malaman jami’a gami da wakilai na wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa.

An gabar da jawabai daban-daban a taron, wadanda suka mayar da hankali kan irin gagarumar gudunmawar day a bayar wajen neman yin gyara a cikin harkar mulkin kama karya da mulukiya na masarautar ‘ya’yan Saud da suka danne komai suka mayar da kasar da azrkinta mallakinsu, al’ummar kasar kuma tamkar bayinsu.

Babban abin da Sheikh Nimr yake magana  a kansa dai shi ne, a yi adalci a tsakanin dukkanin al’ummar kasar Saudiyya, a baiwa al’umma hakkokinta kuma a raba arziki ga ‘yan kasa daidai ba tare da tauye wa wani hakkinsa ba, saboda dalilai na siyasa, ko banbancin mahanga ta akida ko kabilanci.

Kalamansa ba sa yi mahukuntan masarautar dadi, inda suke ganin cewa yin irin wadannan kalamai za su sanya mutane su fahimci inda aka dosa, wanda kuma hakan zai iya tunzura jama’a su mike domin neman hakkokinsu da aka haramta musu a matsayinsu na ‘yan kasa.

شهید باقر النمر، افشاگر خیانت تفکر وهابیت به اسلام / شهادت شیخ نمر نفاق سازمان‌های بین‌المللی را نشان داد

An kama shia  lokuta daban-daban, anda akan yi masa barazana ta kisa, sannan kuma a kwadaitar da shi da abin duniya matukar dai zai shiru da bakinsa, amma sheikh Nimr ya fifita kare hakkin al’ummarsa  akan cin amanarsu, wanda kuma sakamkon hakan makukuntan masarautar ‘ya’yan Saud suka kama shi a cikin shekara ta 2012, kuma fille masa kai da takobi a ranar 2 ga watan janairun 2016.

Malamai sun gabatar da jawabai a wannan taro kan irin zaluncin da aka yi masa, kuma ake ci gaba da yi wa mutanen yankinsa da ke gabashin kasar saudiyya, saboda banbancin mahanga ta akida tsakaninsu da masu mulki, wanda kuma wannan bai kore kasantuwarsu ‘yan kasa masu cikakken hakki kamar kowa ba.

3946925

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: