IQNA

21:50 - January 12, 2021
Lambar Labari: 3485547
Tehran  (IQNA) gwamnatin Qatar ta gina wani katafaren wuri a birnin Doha domin ajiyar tsoffin kayan fasaha na tarihin kasashen musulmi.

An bude wannan wuri ne a cikin shekara ta 2008, amma ya zuwa yanzu ya zama daya daga cikin muhimman wurare da suke daukar hankulan masu yawon bude ido a kasar ta Qatar.

Wurin ajiyar kayan tarihin na fasahar muuslmi na birnin Doha, ya kunshi abubuwa daban-daban na tarihi da suke nuna fasahar musulmi, da suka hada abubuwa na karau da aka yi ayyukan fasaha a kansu, gami da duwatsu masu daraja, da kuma abubuwan da aka samar daga zinariya da azurfa da kuma tagulla.

Wasu daga cikin kayan da ke wurin musulmi sun samar da su ne daruwan shekaru da suka gabata, wasu kuma tun farkon bayyanar musulunci, wasu kuma kafin ma addinin muslunci ya bayyana aka same su a cikin kasashen larabawa.

A halin yanzu akwai abubuwa kimanin 5,400 na tarihi a cikin wannan katafaren wurin ajiyar kayan tarihi na fasahar musulmi da ke birnin Doha, fadin ginin wurin kuma ya kai mita murabba’i dubu 382.

A cikin wurin akwai babban dakin da yake kunshe da wadannan kayayyaki, sai kuma wani babban dakin ayyukan bincike, akwai kuma babban dakin karatu, an kuma gina wurin ne a tsakiyar ruwa.

نگاهی به موزه هنرهای اسلامی دوحه در قطر و ساختمان خاص آن+ فیلم

3945291

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: