IQNA

Human Rights Watch Ta Zargi Faransa Da Kirkiro Sabbin Dokokin Domin Cutar Da Musulmi

22:02 - January 13, 2021
Lambar Labari: 3485552
Tehran (IQNA) Kungiyar Human Rights Watch Ta zargi gwamnatin Faransa da kirkiro sabbin dokoki da nufin galaza wa musulmin kasar.

A wata zantawa da ta yi da kamfanin dillancin labaran AFP babban daraktan gudanarwa na kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch Kenneth Roth ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Faransa tana kirkiro sabbin dokoki wadanda suka yi hannun riga da kare hakkokin dan adam.

Ya ce sabbin dokokin da gwamnatin Faransa ta gabatar da daftarin kudirinsu a halin yanzu, da sunan sabbin dokokin tsaron kasa, suna dauke da wasu bangarori wadanda a zahiri ana nufin take hakkokin musulmi ne a kasar.

Babban daraktan gudanarwa na kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ya ce; gwamnatin Faransa ba ta yi adalci ba, idan ta hada aikin shadanci da kuma imani na akida a matsayin abu guda, domin kuwa bisa dokar kundin tsarin mulkin kasar, dukkanin ‘yan kasa suna hakkin yin aiki da fahimtarsu ta addini.

Tun bayan zanen batunci kan ma’aiki (SAW) da jaridar kasar Faransa ta sake bugawa a watannin baya, wanda ya fuskanci fushin musulmi a duniya baki daya, gwamnatin Faransa ta gabatar da daftarin kudirin wasu sabbin dokoki da za su takura wa musulmi, da sunan aikin tabbatar da tsaron kasa.

 

https://iqna.ir/fa/news/3947456

captcha