IQNA

Biden Zai Ci Gaba Da Bin Siyasar Tilasta Larabawa Kulla Alaka Da Isra’ila

23:21 - January 15, 2021
Lambar Labari: 3485557
Tehran (IQNA) majiyoyin gwamnatin Isra’ila sun ce zababben shugaban Amurka zai ci gaba da bin salon siyasar sanya larabawa su kulla alaka da Isra’ila kamar yadda Trump ya yi.

Shafin yada labarai na arabi 48 ya bayar da rahoton cewa, majiyoyin gwamnatin yahudawan Isra’ila sun bayyana cewa, zababben shugaban Amurka Joe Biden zai ci gaba da bin salon siyasar sanya larabawa su kulla alaka da Isra’ila.

Rahoton ya kara da cewa, Ilyaf Benjamin babban jami’i mai kula da harkokin kasashen yankin gabas ta sakiya a ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ya bayyana cewa, babu batun komawa baya dangane da batun kulla alaka tsakanin Isra’ila da gwamnatocin larabawa.

Ya ce gwamnati mai barin gado a Amurka ta taka gagarumar rawa wajen karkatar da hankulan kasashen larabawa zuwa ga kulla alaka da gwamnatin Isra’ila, haka nan kuma gwamnatin da za ta karbi ragamar mulki za ta ci gaba da bin wannan siyasa.

Ya kara da cewa yanzu haka suna tattaunawa da wasu kasashen arewacin Afirka, da suke shirye su kulla irin wannan alaka da Israila.

Kasashen hadaddiyar daular larabawa da Bahrain da kuma Sudan gami da Morocco, su ne a halin yanzu dai suka sanar da kulla alaka  hukumance da gwamnatin yahudawan Isra’ila bisa matsin lambar gwamnatin Trump mai barin gado.

3947877

 

 

captcha