IQNA

Kwamitin Malaman Musulmi Na Duniya Ya Yi Kira Da A Kawo Karshen Nuna Wariya A Duniya

23:08 - January 16, 2021
Lambar Labari: 3485558
Tehran (IQNA) kwamitin malaman musulmi na duniya ya yi kira da a kawo karshen nuna wariya a tsakanin ‘yan adam.

Jaridar Quds Alarabi ta bayar da rahoton cewa, Ali Qarreh Daghi babban sakataren kwamitin malaman musulmi na duniya ya kirayi dukkanin gwamnatocin kasashen duniya da al’ummomi baki daya da a kawo karshen nuna wariya a tsakanin ‘yan adam a duniya bai daya.

A cikin wani bayani wanda ya wallafa a yau a shafinsa na facebook, babban sakataren kwamitin malaman musulmi na duniya ya bayyana cewa, nuna wariya a tsakanin jinsin ‘yan adam lamari ne da yake tattare da babban hadari ga rayuwar ‘yan adam baki daya, domin kuwa shi ne ke jawo rikice-rikice da tashin hankali har ma da kashe-kashe a wasu lokuta.

Ya ce dukkanin dokoki na addinai da aka saukar daga sama sun hana nuna wariya a tsakanin ‘yan adam, kamar yadda kuma dukkanin dokoki na duniyar yau sun haramta hakan.

Babban sakataren kwamitin malaman musulmin na duniya ya ce; ya zama wajibi a kan dukkanin gwamnatocin duniya da bangarori na al’ummomi da adinai, da su hada karfi da karfe domin kawo karshen duk wani aiki na nuwa wariya da kyamar wani bangare a tsakanin ‘yan adam.

Ya kammala da cewa, abubuwan da suke faruwa a cikin lokutan baya-bayan nan nuna kyama ga musulmi a wasu kasashe sun taka rawa wajen kara yada tsatsauran ra’ayi, domin kuwa ta’addancin da wasu suke danganta addinin musuluni da shi ba gaskiya ba ne, bil hasali ma addinin musulunci yana yakar duk wani nau’i na ta’addanci da zalunci a tsakanin ‘yan adam.

3948161

 

 

 

captcha