IQNA

Gwamnatin Faransa Ta Kulle Masallatai 9 A Kasar

23:10 - January 16, 2021
Lambar Labari: 3485559
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Faransa ta sanar da daukar matakin rufe wasu masallatai guda tara na musulmin kasar.

Shafin yada labaran Raay Media ya bayar da rahoton cewa, hukumomi a Faransa, sun sanar da rufe masallatai guda tara a kasar, a wani mataki da hukumomin kasar suka ce na rashin bin ka’idoji ne.

Mafi yawan masallatan sun kasance a Paris babban birnin kasar.

Wata sanarwar da ma’aikatar cikin gidan kasar ta fitar ta ce an rufe masallatan ne saboda da dalilan da suka hada da ka’idodin tsaro da kuma na gudanarwa.

Matakin dai na zuwa ne makwanni kadan bayan da kasar ta kaddamar da wani aikin sa ido a wuraren ibadar musulmin.

Musulmi a kasar Faransa suna kokawa dangane da irin matakan da gwamnatin kasar take dauka a baya-bayan nan na takura su da sunan dokokin tsaro.

3948157

 

 

captcha