IQNA

Kwamitin Malaman Musulmi Ya Bukaci A Kai Daukin Gaggawa Ga Wadanad Girgizar Kasa Ta Shafa A Indonesia

21:55 - January 18, 2021
Lambar Labari: 3485565
Tehran (IQNA) kwamitin malaman musulmi na duniya ya bukaci da a kai daukin gaggawa ga wadanda girgizar kasa ta rutsa da sua  kasar Indonesia.

Kamfanin dillancin labaran anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da kwamitin malaman musulmin ya fitar, ya bayyana cewa kai daukin gaggawa ga al’ummar Indonesia da hatsarin girgizar kasa ya rutsa da su yana daga cikin muhimman ayyuka na alhairi da ya kama musulmi su yi gaggawa wajen aikatawa.

A safiyar ranar jumma’a ce girgizar kasa mai karfin ma’aunin richter 6.2 ta aukawa tsibirin Sulawesi na kasar Indonesia, inda ta rusa gine-ginen a asibitin birnin Mamuju kan marasa lafiya da jami’an jinya da suke cikinsa.

Rahotannin sun kara da cewa akalla mutane talatin da hudu ne aka tabbatar da mutuwarsu ya zuwa lokacin da abin ya faru, amma daga bisani adadin ya ci gaba da karuwa.

Jami’an jinya a kasar sun fara bincike don gano wadanda suke da sauran shan ruwa a wurare daban-daban a tsibirin.

Ali Rahaman wani jami’in kungiyar bada agaji a birnin Mamuju ya bayyana cewa yawan wadanda suka mutu zai karu don har yanzun suna neman wasu mutane da dama wadanda ba’a suka bace a cikin burbushin gine-ginen da suka rushe.

 

3948243

 

 

 

captcha