IQNA

A Karon Farko Za A Fara Koyar Da Darasi Mai Suna Harshen Kur’ani A Jami’a A Kasar Australia

22:44 - January 23, 2021
Lambar Labari: 3485580
Tehran (IQNA) za a fara koyar da wani darasi mai suna harshen kur’ani a jami’ar birnin Sydney na kasar Australia.

Shafin yada labarai na tashar SBS Arabic24 ya bayar da rahoton cewa, Ali Yunus Dahsh, wani malamin yaruka  ajami’ar birnin Sydney a kasar Australia ya bayyana cewa, za a fara koyar da darasi mai suna harshen kur’ani a wannan jami’ar, a bangaren harsuna.

Malamin ya ce wannan darasi zai kebanci masu koyon harshen larabaci ne, inda za a kara wannan darasi a cikin darussansu a wannan jami’a, da nufin kara karfafa fahimtarsu da harshen larabci.

Ya ci gaba da cewa wannan shi ne karon farko a tarihin kasar Australia da za a fara koyar da wannan darasi, wanda kuma ta hanyar hakan daliban za su iya fahimtar ma’anonin ayoyin kur’ani mai tsarki kamar yadda suke a cikin harshen larabaci.

Akwai dalibai da dama a kasar Australia da suke koyon harshen larabci a jami’a, wadanda akasarinsu suna koyon harshen ne domin ya taimaka musu a wasu ayyukansu ad suke gudanarwa, ko kuma suke da burin gudanarwa, ko kuma ayyuka na bincike da ya shafi addinin muslunci ko kasashen larabawa da tsoffin al’adunsu.

3949219

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :