IQNA

19:00 - February 22, 2021
Lambar Labari: 3485680
Tehran (IQNA) Iyalan fitaccen dan gwagwarmayar kare hakkokin bakaken fata a kasar Amurka Malcolm X sun bukaci da a sake dawo da batun bincike kan musabbabin mutuwarsa.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a wani taron manema labarai da ta yi a jiya a taron tunawa da cikar shekaru 55 da kisan mahaifinta, ta bayyana cewa a matsayinsu na iyalansa, suna bukatar a sake dawo da batun bincike kan kisan gillar da aka yi masa.

Wannan na zuwa dai bayan samun wasu bayanai da ke nuni da cewa, akwai hannun jami’an ‘yan sanda na birnin New York da kuma na hukumar tsaro ta FBI wajen kisan Malcolm X.

Bangarori na shari’a a New York sun sanar da cewa, sun fara gudanar da wani sabon bincike kan wannan batu, domin gano hakikanin abin da ya faru dangane da kisan Malcolm X.

A taron manema labarai da iyalan Malcolm X suka gudanar a jiya, sun karanta wasikar da wani tsohon jami’in ‘yan sanda na birnin New York mai suna Raymond Wood ya rubuta, wanda ya rasu a shekarun baya, inda ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda na New York da kuma jami’an FBI ne suka kashe Malcolm X.

Wood ya kasance dan sanda ne bakar fata, ya bayyana a cikin wasikar tasa cewa, bisa umarnin na sama da shi, ya shiga cikin jama’ar Malcolm X domin yin aikin leken asiri, da kuma sanin hanyoyin da za a kashe shi, kuma daga karshe abin da ya faru kenan.

Shekaru 55 da suka gabata a ranar 21 Febrairu shekara ta 1965, wasu mutane uku suka bude wutar bindiga  a kan Malcolm X, ko kuma Hajj Malik Al-shabbaz sunan da aka sanya masa bayan ya musulunta, a  lokacin da yake gabatar da wani jawabi a Audubon a cikin New York, inda  a nan take ya rasa ransa.

A cikin watan Febrairun shekarar 2020 da ta gabata ce kamfanin Netflix ya watsa wani fim mai taken wa ya kashe Malcolm X, daga lokacin ne kuma lauyoyi suka fara neman a sake dawo da batun gudanar da bincike kan yadda aka kashe shi da kuma wadanda suke da hannu a kisan nasa.

3955502

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: