IQNA

Tsohon Jakadan Amurka A Najeriya:
20:03 - February 28, 2021
Lambar Labari: 3485698
Tehran (IQNA) Tsohon jakadan Amurka a Najeriya ya bayyana cewa, za a iya magance da dama daga cikin matsaloli na tsaro a wasu kasashen Afirka ta hanyar gyara na tattalin arziki.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna, Tsohon jakadan Amurka a tarayyar Najeriya John Campbell ya bayyana cewa, za a iya magance da dama daga cikin matsaloli na tsaro a wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka ta hanyar yin gyara na tattalin arziki da kuma bangaren siyasa.

Ya ce ba kowane lokaci ne daukar mataki na soji ko yin amfani da karfi yake zama hanyar kawo karshen matsalar tsaro ba, a wasu lokuta a kan yi la’akari da yanayi domin daukar wasu matakan na daban, wadanda za su taimaka domin magance irin wadannan matsaloli.

Dangane da matsalolin tsaro da suke da alaka da kungiyoyin ‘yan bindiga masu tsatsauran ra’ayin salafiyya a cikin wasu yankuna na kasashen yammacin Afirka, ya bayyana cewa akwai abubuwa da dama da suke haddasa hakan.

Ya ce daga ciki har da matsaloli na siyasa da kuma kutsen kasashen ketare a cikin wadannan kasashe, a wasu lokuta domin cimma burin a siyasa, amma kuma hakan sau tari yakan koma ne ga rauni na gwamnatocin kasashen.

Yin Gyara Ta Fuskar Siyasa Da Tattalin Arziki Zai Taimaka Wajen Magance Matsalar Tsaro A Afrika

Ya ci gaba da cewa, wadannan kasashen suna samun karuwar jama’a a kowane lokaci, amma kuma babu wani tsari na tafiyar da jama’ar da kuma sama mata makoma, saboda haka rashin tsari kan iya haifar da matsaloli masu tarin yawa a cikin kowace al’umma, daga ciki kuwa har da na tsaro.

Baya ga haka kuma ya bayyana matsalolin tattalin arziki da cewa, su kan zama asasi na rashin tsari a wasu lokuta a cikin al’umma, ta yadda gwamnatoci ba su iya samar da hanyoyin da za su iya wadata mutane da abubuwan da suke bukata na rayuwa, kama daga ayyukan yi, ko samar da hanyoyin da za su kawo ayyukan yi ga jama’a musamman ma matasa.

Ya ce za a iya ganin hakan a wasu daga cikin kasashen yammacin Afirka wadanda matsalolin tsaro suka yi wa katutu, kamar Najeriya, Nijar, Chadi da Mali, duk kuwa cewa yanayin a Najeriya yana da banbanci da sauran kasashen, bisa la’akari da arzikin da kasar take da shi, to amma dogaro da abu daya wato danyen man fetur, yana haifar wa kasar matsaloli masu tarin yawa.

A nan za a iya cewa rashin tsari ne ya yi tasiri wajen haifar da matsaloli na tsaro a Najeriya, domin kuwa za a iya yin amfani da hanyoyi daban-daban na bunkasa tattalin arzikin kasar tare da samar da ayyukan yi ga matasa, da kuma sanya ido a kansu domin kada su fada cikin yaudarar kungiyoyi masu tsatsarun ra'ayi da ke kai matasa zuwa ga fadawa cikin ta'addanci da sunan addini, ko kuma su fada cikin ta'addancin da sunanan wasu abubuwa na daban, wanda yake haifar da babbar matsalar tsaro ga al'ummar kasa.

 

3956413

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: