IQNA

20:17 - February 28, 2021
Lambar Labari: 3485699
Tehran (IQNA) majalisar dinkin duniya ta yi Allawadai da kakkausar murya kan sace yara 'yan mata 'yan makarantar kwana a cikin jihar Zamfara da ke Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya fitar, wanda mai magana da yawunsa ya karanta, ya bayyana cewa sace-sacen yara 'yan makaranta da ake yi a Najeriya abin ban takaici ne da Allawadai.

Guterres ya ce, abin da yake faruwa na sace yara 'yan makaranta a Najeriya da ma kai wa mutane hare-hare da karkashe su, da ma yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, dukkan wadannan ayyuka ne na ta'addanci, da keta hurumin dan adam.

Ya ce majalisar dinkun duniya tana nuna cikakken goyon bayanta ga al'ummar Najeriya, sannan tana kira ga gwamnatin kasar da ta dauki matakan da suka dace domin fuskantar irin wannan lamari, da kuma tabbatar da cewa an kamo masu aikata irin wadannan ayyukan domin su fuskanci hukunci a gaban kuliya.

3956640

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: